logo

HAUSA

Majalissar kolin soji a Nijar ta jingine kundin tsarin mulkin kasar

2023-07-29 16:34:44 CMG Hausa

An ayyana tsohon shugaban rundunar dake gadin fadar shugaban kasar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani, a matsayin shugaban majalissar tsaron kasa ko CNSP, biyowa bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar dake yammacin Afirka. 

Kafar talabijin ta kasar ce ta sanar da hakan a jiya Jumma’a, kana daga bisani Tchiani ya sanya hannu, kan dokar jingine kundin mulkin kasar, tare da rushe gwamnati. Kaza lika ya ayyana baiwa CNSPn karfin ikon doka, na kafawa da zartas da dokokin gudanar da mulki, yayin da zai ci gaba da kasancewa shugaban majalisar zartaswar, mai wakiltar kasar a dukkanin huldodin kasa da kasa.

To sai dai kuma kasashen duniya da dama na ci gaba da bayyana damuwa, game da yanayin da ake ciki a jamhuriyar ta Nijar. 

A jiya Juma’a, kwamitin tsaron MDD ya yi matukar Allah wadai da juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum. Kwamitin ya bayyana takaicin abun da ya auku a kasar, wanda a cewar sa tarnaki ne ga kokarin da ake yi na kyautata sha’anin jagoranci, da wanzar da zaman lafiya a kasar.

Ita ma a nata bangare, gwamnatin Afirka ta kudu, ta fitar da sanarwa kan batun, inda ta ce kasar na matukar adawa, da kwace mulki da karfin tuwo daga ko wane bangare na Nijar, kasancewar hakan zai mayar da hannun agogo baya, game da nasarorin da aka samu karkashin mulkin dimokaradiyya, da ci gaban kasa, kuma hakan barazana ne ga burin da ake da shi na bunkasar nahiyar Afirka.

A nasa bangare kuwa, shugaba William Ruto na Kenya, cewa ya yi sauya gwamnati ta hanyar da ba ta dimokaradiyya ba, haifar da koma baya ne ga nasarorin da aka cimma tsawon shekaru a kasashen Afirka. (Saminu Alhassan)