logo

HAUSA

Ina dalilin da ya sa Amurka ta hura wutar rikici game da “yin takara a sararin samaniya” tare da kasar Sin a Argentina?

2023-07-29 21:06:49 CMG Hausa

Shugaban hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Amurka Bill Nelson, ya ziyarci kasar Argentina a ranar 27 ga watan nan, inda a wajen wani taron manema labarai da aka yi a birnin Buenos Aires, Nelson ya ayyana nasarorin da kasar Sin ta samu wajen binciken duniyar wata, da duniyar Mars, tare da bayyana cewa, a halin yanzu Sin da Amurka suna yin takara kan harkokin sararin samaniya.

Wannan ba shi ne karon farko da manyan jami’an Amurka, suke hura wutar rikici kan batun sararin samaniya a kasar Argentina ba. A watan Maris din shekara ta 2022 ma, kwamandar rundunar sojojin Amurka dake kudancin kasar wato USSOUTHCOM, Laura Richardson, ta ziyarci Argentina, inda ta ce tashar binciken sararin samaniya mai nisa ta hadin-gwiwar Sin da Argentina dake jihar Neuquén, tasha ce ta aikin soja.

To sai dai a nasa bangare, ministan kula da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na Argentina Daniel Filmus, ya maida martani kan wannan furuci na Laura, inda ya ce, kasarsa na amfani da tashar dake jihar Neuquén don gudanar da hadin-gwiwa tare da kasar Sin ne a fannin binciken sararin samaniya da taurarin dan Adam, kamar yadda kasar take yi da kasashen Turai.

Hakikanin gaskiya, tun a shekara ta 2012, hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta Turai, ta kafa tashar binciken sararin samaniya mai nisa a Argentina, amma ko me ya sa Amurka ke zargin kasar Sin ita kadai?

Tun dai lokacin fara binciken harkokin sararin samaniya ya zuwa yanzu, kasar Sin na tsayawa kan fannin zaman lafiya. Kamar tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin da a yanzu haka take aiki a sararin samaniyar, wadda aka bude ga dukkan kasashe membobin Majalisar Dinkin Duniya, wanda hakan ya zama karon farko a tarihi na yin hakan. Wannan ya shaida niyyar kasar Sin na binciken sararin samaniya, wanda ba za’a iya shafa mata bakin fenti kan sa ba.

Sararin samaniya, gida ne ga daukacin al’ummar duniya, ba wai wuri ne da wata kasa ke iya nuna fin karfinta ba. Kaza lika bai kamata wasu Amurkawa, su rike tsoffin ra’ayoyinsu na da ba, kuma bai kamata a maimaita ayyukan lokacin yakin cacar baka ba, wannan ba zai yiwu ba. (Murtala Zhang)