logo

HAUSA

’Yan Nijar mazauna kasashen waje sun fara muhawara kan makomar kasar bayan juyin mulki

2023-07-28 09:13:11 CMG Hausa


’Yan Nijar mazauna kasashe makwafta sun fara muhawara kan makomar kasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Larabar da ta gabata, da yawansu na fargabar rashin tabbas na kokarin farfado da tattalin arzikin kasar da shugaba Muhammadu Bazoum ya kudiri aniya.

A yayin wani taro da suka gudanar a Kano wasu daga cikin ’yan jamhuriyyar Nijar sun ce hannun agagog zai iya komawa baya a kan gwadaben ci gaban da hambararriyar gwamnatin damokradiya ta fara dora kasar a kai, ko da yake wasu na da mabambantan ra’ayi a kan juyin mulkin.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Da yawa wasu ’yan jamhuriyyar ta Nijar mazauna Najeriya sun yi imanin cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Bazoum ya kamo hanyar dora kasar kan kyakkyawar turba da za ta kai ga bunkasuwar tattalin arziki, ilimi, tsaro da zamantakewar al’ummar kasar.

Sun yi bayanin cewa Jamhuriyyar Nijar kasa ce mai rauni gaske ta fuskar tattalin arziki wadda kuma ba ta bukatar yawan katsalandan daga wasu da manufarsu ta sha bamban da masu akidar ci gaba.

Alhaji Abdullahi Idris shi ne mataimakin shugaba na kasa a Najeriya na jam’iyyar PNDS tarayya ya ce hakika a yanzu zai yi wahala a iya kiyasta asarar da jamhuriyyar Nijar za ta yi sakamakon wannan juyin mulki.

“Tabbas tsohon shugaba Bazoum ya dora Nijar kan kyakkyawar turba, inda ba a yi wannan juyin mulki ba har ya samu ya kai karshen wa’adin mulkinsa ’yan Nijar za su yi mamakin ci gaban da kasar za ta samu domin kuwa ya tanadi abubuwa da dama wadanda za su saukakawa talakawan kasar, domin kafin zuwa Bazoum Nijar ba ta cikin kasashe masu arziki, amma zuwa sa yanzu an saka kasar kan jerin kasashen da suke da hasken ci gaban tattalin arziki a duniya.”

“Suna na Zara`u ’yar Nijar mazauniyar Najeriya, gaskiya wanann juyin mulki ba mu ji dadi ba, abun ya sosai mana rai.”

“Ya kamata shugabannin na Nijar su yi karatun ta nutsu, juyin mulki ba yanzu aka fara ba a Nijar, Ba’are mai nasara ransa ya rasa a irin wanann juyin mulki. Ya kamata a ce lokacin Bazoum ya zo ya yiwa talakawan Nijar abun da ransu ya fi so maimakon abin da ranka yake so, to wannan aya ce ga shugaba mai zuwa a nan gaba.”

Wasu ’yan kasar Nijar ke nan mazauna Najeriya lokacin da suke baiyana ra’ayoyinsu game da juyin mulki da sojoji suka yi. (Garba Abdullahi Bagwai)