logo

HAUSA

Sojoji sun bayyana Abdourahamane Tchiani a matsayin sabon shugaban jamhuriyar Nijar

2023-07-28 21:12:36 CMG Hausa

Rundunar sojojin dake tsaron fadar shugaban kasar Nijar, ta ayyana Janar Abdourahamane Tchiani, a matsayin sabon shugaban majalissar kolin tsaron kasa, biyowa bayan juyin mulkin soji a kasar, kamar dai yadda kafar talabijin ta gwamnatin kasar ta bayyana a Jumma’ar nan.

Tun a daren ranar Laraba ne dai rundunar tsaro da kare kasa ta FDS, ta gabatar da sanarwar kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, bayan shafe ‘yan sa’o’i suna tsare da shugaban kasar.

Da yake bayani don gane da dalilan kifar da gwamnatin Bazoum, mamba a rundunar ta FDS Kanal Manjo Amadou Abdramane, ya ce ci gaba da tabarbarewar yanayin tsaro, da tattalin arziki, da gazawar jagoranci na gari ne ya haifar da juyin mulki.   (Saminu Alhassan)