logo

HAUSA

Shugaban Nijeriya ya mika sunayen mutane 28 da yake son nadawa ministoci

2023-07-28 10:33:56 CMG Hausa

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya mika jerin sunayen mutane 28 da yake son nadawa ministoci, ga majalisar datattwan kasar domin neman amincewarta.

Bisa tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya kamata shugaban kasa ya mika sunayen wadanda yake son nadawa ministoci cikin kwanaki 60 bayan ya sha rantsuwar kama aiki.

Shugaban majalisar dattawan Godswill Akpabio ya tabbatar da karbar jerin sunayen, inda ya karanta shi yayin zaman majalisar na jiya Alhamis.

A cewar Godswill Akpabio, daga cikin sunayen, akwai ’yan jam’iyyar adawa, abun ya dace da alkawarin da shugaban ya yi na gina gwamnatin hadin kan kasa mai kwarewa.

Shugaba Tinubu ya kuma sanar da majalisar cewa, zai aike da karin sunaye nan ba da jimawa ba. (Fa’iza Mustapha)