logo

HAUSA

Najeriya ta yi kira da a inganta amfani da harsunan asali

2023-07-28 11:57:14 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne wani babban jami’in ma’aikatar ilimi ya ce, gwamnatin Najeriya za ta inganta amfani da harsunan asali wajen sadarwa, musamman a matakin farko.

Babban sakataren ma’aikatar ilimi David Adejo ne ya bayyana hakan a wani shiri da aka gudanar a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya a ranar Alhamis din nan, inda ya ce wannan yunkuri na nufin kara zaburar da sha’awar yara wajen koyon harsunan asali domin gujewa batar asali da riko da dabi’un al’adu na musamman.

A cewar Adejo, yin magana da harshen asali na daukaka da yayata kyawawan dabi’u na magabata ba wai kawai nuna asalin mutum ba.

Jami’in ya ce, ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin mutum ko al’umma yawanci yana da alaka da amfani da harshensa na asali.

Ya yi kira da a inganta da kuma kare harsunan asali ta hanyar ingantattun manhajoji na makarantu da tsare-tsare masu inganci. (Yahaya Babs)