logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da shugaban Turkiye

2023-07-27 09:26:52 CMG Hausa

Darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwmainis ta kasar Sin (JKS) Wang Yi, ya gana da shugaban kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan a birnin Ankara na kasar Turkiye jiya Laraba.

Wang ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan Turkiye wajen kiyaye ‘yancinta da bin hanyar samun bunkasuwa da ta dace da yanayin kasarta. Jami’in na Sin wanda ya kai ziyarar yini guda a kasar Turkiye, ya kuma tattauna da ministan harkokin wajen kasar Hakan Fidan.

Wang ya kara da cewa, Sin za ta yi aiki tare da Turkiye wajen mayar da hankali da zurfafa amincewa da juna a fannin siyasa, a wai mataki na inganta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare shugaba Erdogan ya bayyana cewa, kasashen Turkiye da Sin, kasashe ne dake da tasiri a duniya, kuma fa’idar alakar kasashen biyu, ta zarce tsakaninsu kadai. (Ibrahim)