logo

HAUSA

Sabon hali da kasar Nijar ta shiga bayan da sojoji suka kwace mulkin kasar

2023-07-27 17:59:41 CMG Hausa

A Nijar, an wayi gari a ranar jiya 26 ga watan Yulin shekarar 2023 cikin rudanin juyin mulki. Rahotanni na cewa, an kifar da mulkin shugaba Mohamed Bazoum, tare da tsare shi. Wajen karfe goma sha daya na daren jiya, manyan sojoji na kwamitin kasa domin kiyaye da ceton kasa CNSP sun yi sanarwa a gidan talabijin na kasa domin tabbatarwa ’yan kasa da duniya juyin mulkin.

Yanzu cikin wani hali kasar Nijar ta shiga bayan da sojoji suka kwace mulki, ga rahoton de abokin aikinmu Mamane Ada da yanzu haka yake a birnin na Yamai ya kawo mana.