logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira da a hana rikici tsakanin Rasha da Ukraine ta’azzara

2023-07-27 10:56:18 CMG Hausa

 

A jiya Laraba 26 ga wata ne kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da tarukan jama'a guda biyu kan rikicin Rasha da Ukraine. Kasar Sin ta bayyana cewa, ya zama tilas a hana al'amura kara ta'azzara, da magance tasirin rikicin, da sa kaimi ga warware rikicin ta hanyar siyasa.

Geng Shuang, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya bayyana a gun taron cewa, rikicin na ci gaba da ta’azzara a kasar Ukraine, fadace-fadacen na ci gaba da karuwa, yayin da aka ci gaba da rasa rayukan fararen hula. Sin ta damu matuka game da lamarin. Geng Shuang ya bayyana cewa, ya zama wajibi a sassauta wa jama'a radadin da suke ciki, tare da hana lamarin ci gaba da ta’azzara.

Geng Shuang ya jaddada cewa, yarjejeniyar fitar da kayayyakin amfanin gona daga tashar jiragen ruwa na Bahar Asuwad, da yarjejeniyar fahimtar juna game da fitar da hatsi da takin kasar Rasha, na taka muhimmiyar rawa wajen daidaita farashin abinci a duniya, da tabbatar da samar da abinci a duniya, musamman inganta samar da abinci ga kasashe masu rauni. Har yanzu akwai damar sake dawowa da yarjejeniyar. Ya kamata kasashen duniya su inganta bangarorin da za su karfafa tattaunawa da tuntubar juna, da himmantuwa wajen kulawa da juna, da yunƙurin dawo da fitar da hatsi da takin zamani daga Rasha da Ukraine da wuri. (Yahaya)