logo

HAUSA

Guterres ya yi tir da yunkurin juyin mulki a Niger

2023-07-27 10:01:17 CMG Hausa

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi suka da kausasan kalamai kan yunkurin juyin mulki a jamhuriyar Niger.

Cikin wata gajeriyar sanarwa a jiya, Antonio Guterres ya ce yana bibiyar abun dake faruwa a kasar. Kuma yana kakkausar suka ga duk wani yunkuri na kwace iko da karfi da kuma kawo cikas ga gwamnatin demokradiyya da zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar ta Niger.

Rahotanni sun ce sojojin rundunar tsaron shugaban kasa sun rufe shugaban a fadarsa a wani yunkuri dake bayyana tawaye.

An yi garkuwa da shugaban kasar Mohamed Bazoum da iyalinsa a gidansa dake fadar shugaban kasa a birnin Yamai, bayan an tsayar da yarjejeniyar da shugaban rundunar sojin tsaron shugaban.

Da yammacin jiya Laraba, agogon kasar ne, sojojin da suka tsare shugaban suka bayar da sanarwa ta gidan talabijin na kasar, inda suka bayyana cewa an hambarar da shugaba Bazoum, kana suka ayyana dokar hana fita daga karfe 7 na yamma zuwa 5 na yammacin yau Alhmis, tare da rufe iyakokin kasar. (Fa’iza Mustapha)