logo

HAUSA

An alakanta yawaitar mutuwar mata masu juna a jihar Adamawa bisa yawaitar kwalejojin kiwon lafiya marasa inganci

2023-07-27 10:19:21 CMG Hausa

 Majalissar dokokin jihar Adamawa ta bayyana damuwarta kan ci gaba da karuwar kwalejojin koyar da aikin kiwon lafiya da ba su da cikakkun takardun izinin gudanarwa a jihar.

A zaman da ta gudanar jiya Laraba 26 ga wata, majalissar ta ce irin wadannan kwalejoji suna yaye baragurbin dalibai da suke sanadiyar asarar rayuka musamman na mata masu juna biyu, wanda bincike ya tabbatar da cewa a duk shekara ana asarar rayukan irin wadannan mata har 636 a jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Dan majalissar mazabar Mubi ta kudu Hon Yohanna Sahabo Jauro shi ne ya tashi ya gabatar da kudurin gaggawa a zauren majalissar na neman a baiwa kwamatin lafiya damar gudanar da bincike a kan yadda makarantu masu zaman kansu dake bayar da horon kiwon lafiya a jihar ke gudanar da ayyukansu.

Kamar yadda ya fada a yanzu haka a jihar ta Adamawa akwai irin wadannan kwalejoji har kusan 19 da suke gudanar da harkokinsu ba da sanin hukuma ba, kuma suna ci gaba da yaye dalibai da suke zaman hadarin gaske ga ci gaban lafiyar al’ummar jihar.

“Da yawa daga cikin wadannan kwalejoji ba su da ingancin da ya kamata, sannan kuma tsarin darussa da aiyukan da suke yi, ko kadan babu sahalewar hukumomin da suka kamata, wasunsu ma a cikin ajujuwan makarantun firamaren gwamnati suke bayar da horo da yamma idan an tashi dalubai,  a don haka nake neman majalissar da ta duba wannan al’amari cikin gaggawa domin batun kiwon lafiya ba batu ne da ya kamata a yi wasa da shi ba.”

Bayan doguwar muhawara da ’yan majalissar suka gudanar, daga bisani shugaban majalissar dokokin jihar ta Adamawa Hon Bathiya Wesley ya umarci kwamitin lafiya na majalissar da ya binciki al’amari tare da kawo wa majalissar rahotonsa cikin makonni biyu masu zuwa. (Garba Abdullahi Bagwai )