logo

HAUSA

Yuyin mulki: Sojojin sun karbe iko a kasar Nijar

2023-07-27 10:04:24 CMG Hausa

A Nijar, an wayi gari a ranar jiya 26 ga watan Yulin shekarar 2023 cikin rudanin juyin mulki. Rahotanni na cewa, an kifar da mulkin shugaba Mohamed Bazoum, tare da tsare shi. Wajen karfe goma sha daya na daren jiya, manyan sojoji na kwamitin kasa domin kiyaye da ceton kasa CNSP sun yi sanarwa a gidan talabijin na kasa domin tabbatarwa ’yan kasa da duniya juyin mulkin.

Daga birnin Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya turo mana da rahoto. 

Wadannan manyan sojoji su goma ne suka bayyana a gidan talabijin na kasa, kuma kanal manjo Amadou Abdramane ya karanto sanarwar ta kwamitin CNSP. Sanarwar tana mai cewa, “Dunkule a cikin kwamitin kiyaye da ceto kasa na CNSP mun dauki niyyar kawo karshen ikon da kuka sani, wannan kuma bayan la’akari da ci gaba da tabarbarewar matsalar tsaro, rashin jagoranci mai kyau ta fuskar tattalin arziki da jama’a. Mun jaddada yardarmu wajen girmama dukkan alkawuran da kasar Nijar ta dauka kuma ta rattabawa hannu. Muna tabbatarwa gamayyar kasa da kasa cewa za mu girmama ’yanci da kariyar jikin shugabannin da aka ma juyin mulki kamar yadda dokokin ’yancin dan adam suka tanada.”

Haka kuma, sojojin sun bayyana dakatar da mulkin jamhuriya ta 7, don haka sakatarorin ofisoshi da na ministoci za su ci gaba da tafiyar da harkoki da ayyukan kasa, jami’an tsaro na FDS su kuma za su rike nauyin kula da matsalar, haka kuma sojojin da suka yi juyin mulkin din sun yi kashedi da bukatar dukkan abokan huldar Nijar da kasashen waje da kada su tsoma bakinsu.

Haka zalika, sabbin shugabannin kasar Nijar, sun dauki matakin rufe iyakokin sama da kasa har zuwa lokacin daidaituwar al’amura, haka kuma sun ayyana dokar ta bace tun daga ranar yau daga karfe goma na dare har zuwa karfe biyar na safe a dukkan fadin kasa har zuwa wani sabon umurni, in ji kanar manjo Amadou Abdramane a sanarwar ranar yau 26 ga watan Yulin shekarar 2023 a Yamai. Sanya hannun shugaban kwamitin kiyaye da ceto kasa na CNSP.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.