logo

HAUSA

Kungiyoyin AU da ECOWAS sun yi tir da juyin mulki a Nijar

2023-07-27 15:20:54 CMG Hausa

A jiya 26 ga wata ne sojojin Nijar da suka yi juyin mulki suka fitar da wata sanarwa ta gidan talabijin na kasar Nijar cewa sun hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum na Nijar.

Da yammacin ranar kuma, shugaban hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat, ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana hakan a matsayin "cin amanar kasa" tare da yin kira ga sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar da su kawo karshen wannan dabi'ar da ba za a amince da ita ba cikin gaggawa. Hukumar ECOWAS ita ma ta fitar da sanarwa ta kafafen sada zumunta na yanar gizo inda ta yi kira da a gaggauta sakin shugaban da ake tsare da shi ba tare da wani sharadi ba.

Rahotanni sun bayyana cewa Bola Tinubu, shugaban riko na kungiyar ECOWAS, kana shugaban kasar Najeriya, ya gana da Patrice Talon, shugaban kasar Benin a Abuja, babban birnin Najeriya, a ranar 26 ga wata. Kungiyar ECOWAS za ta tura Talon zuwa Nijar domin shiga tsakani. (Yahaya)