logo

HAUSA

An yi taro na 77 na kwamitin binciken harkokin kudi na MDD

2023-07-27 11:38:53 CMG Hausa

Kwamitin binciken harkokin kudi na MDD, ya gudanar da taro karo na 77, daga ranar 25 zuwa 26 ga wannan wata, a hedkwatar majalisar dake birnin New York na Amurka, inda shugaban kwamitin kuma shugaban hukumar binciken harkokin kudi ta kasar Sin, Hou Kai ya shugabanci taron.

A yayin taron, an yi bincike tare da zartas da rahotanni 21 game da hukumomin da ayyukan kwamitin ya shafa a shekarar 2022. Haka zalika, membobin kwamitin sun yi shawarwari da babban sakataren MDD António Guterres, inda suka yi musayar ra’ayoyi game da matsalolin da aka gano a yayin binciken shekarar 2022 da ayyukan dake gaban komai da kulabalen da ake fuskanta da sauransu.

Hou Kai ya jaddada cewa, MDD ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwar dan Adam, yana mai cewa ana bukatar raya MDD mai karfi yayin da ake kokarin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama. Kuma kwamitin binciken harkokin kudi na majalisar zai sauke nauyin dake wuyansa don sa kaimi ga cimma ajandar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030 ta MDD.

A nasa bangare, Antonio Guterres ya yabawa kwamitin bisa muhimmiyar rawar da ya taka a fannonin kyautata tsarin sarrafa harkokin MDD, da daidaita matsalolin da take fuskanta da sauransu. Ya kara da cewa, za a kara hadin gwiwa da kwamitin don gano matsalolin da suka shafi harkokin kudi da daidaita su yadda ya kamata. (Zainab)