logo

HAUSA

Kaso 43 na kananan yara ne ke cikin kangin bauta a tarayyar Najeriya

2023-07-26 09:30:56 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce a kalla kaso 43 na yaran kasar da shekarun ke tsakanin 5 zuwa 11 ne ke fuskantar kangin bautarwa.

Babbar sakatariya a ma’aikatar kodago da nagartar aiki na kasar Mrs Kachollom Daju ce ta tabbatar da hakan a farkon wannan mako yayin wani tattaki da aka gudanar a birnin Abuja a wani bangare na bikin ranar yaki da al`adar bautar da kananan yara na 2023, bautar da ta kunshi tallace-tallace da aikin wahala.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Madam Kachollom Daju ta ce batun bautar da kananan yara ya kasance babban abun damuwa a Najeriya, kasancewar yana take hakkin kananan yara wajen neman ilimi da kuma kyautata sha’anin tunaninsu da tarbiya.

Babbar sakatariyar ma’aikatar kodago ta tarayyar Najeriya ta ci gaba da cewa, wannan  kaso na kananan yaran da bincike ya tabbatar ana bautarwa, hakika yana bukatar shigowar masu ruwa da tsaki domin yiwa tunfkar hanci ta hanyar kawar da wannan munmunar al’ada a kasar da ma duniya baki daya.

Wannan muryoyin wasu kananan yara mata ne da na ci karo da su suna talla a birnin Kano, cikin kunya sun shaida mun cewa suna yi talla ne domin samun kudin da za su biya bukatun kansu kasancewar iyayensu ba su da karfin daukar dawainiyarsu gaba daya.

“Wani lokaci ba mu da kudin kashewa, wanda da kudin talla ne muke samun sayen sabulun wanki da na wanka, sannan kuma ina tanadin amfani da ribar tallar wajen sayen kayan daki idan aure na ya zo.”

“Kudi ne ba mu da shi ya sa muke talla, kuma da kudin tallar muke taimakawa iyayen mu wajen yi mana dinkin salla ko na bikin mauludi, ko da yake wani lokaci mahaifin mu yana bakin kokarinsa amma muna taimaka masa idan ya gaza, da kudin tallar muke sayen hijabi da takalman sakawa.”

Malam Shehu Abdullahi shi ne babban jami’in hukumar kare hakkin dan adam na tarayyar Najeriya shiyyar Kano ya shaida mun cewa a bara kadai ofishinsu ya karbi korafin keta hakkin dan adam har 1500 ya yi da kaso 5 daga cikin wannan adadi kuma ya shafi bautar da kananan yara ne.

“A bangare na arewacin Najeriya za ka ga cewa hakika matsalolin kananan yara kamar bautar da su ya ta’azzara sosai, ko da yake wanann al’amari ya shafi kowanne bangare na kasa, sai dai mu a nan arewacin Najeriya ya fi tasiri sosai wajen rayuwar yaran, musamman za ka ga irin wadannan yara a kan tituna suna talla ko wani aiki da ya fi karfin tunaninsu, wanda hakan laifi ne babba wanda kuma hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa tana iyakacin bakin kokarin gudanar da dukkan bincike domin samar da yanayin da za a kawo karshen wanann halayyar ta bautar da kananan yara a kasa baki daya.” (Garba Abdullahi Bagwai )