logo

HAUSA

Hasashen IMF ya nuna tattalin arzikin duniya zai yi tafiyar hawainiya zuwa kaso 3.0 a shekarar 2023 da ta 2024

2023-07-26 10:30:07 CMG Hausa

 

Asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya yi hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya zai yi tafiyar hawainiya, inda zai sauka daga kimanin kaso 3.5 a shekarar 2022, zuwa kaso 3.0 a shekarar 2023 da ta 2024. Sai dai hasashen ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, bai sauya daga kaso 5.2 a shekarar 2023 da kaso 4.5 a shekarar 2024 ba.

Sabon hasashen da asusun IMF ya fitar a jiya ya ce, yayin da hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya na shekarar 2023 ya wuce wanda aka yi a watan Afrilun bana kadan, har yanzu ba shi da kwari idan aka waiwayi tarihi. IMF ya kara da cewa, manufofin da manyan bankuna ke dauka don yaki da hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da kara matsi kan harkokin tattalin arziki.

Ana sa ran matakin hauhawar farashin kayayyaki a duniya ya sauka daga kaso 8.7 da ya kasance a shekarar 2022, zuwa kaso 6.8 a bana da kuma kaso 5.2 a shekarar 2024. (Fa’iza Mustapha)