logo

HAUSA

Shugaban Afrika ta Kudu ya tattauna da Wang Yi ta wayar tarho

2023-07-26 14:02:03 CMG HAUSA

 

Jiya Talata, shugaban kasar Afrika ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa wanda ke ziyarar aiki a wasu sassan kasar ya tattauna da Wang Yi, darektan ofishin harkokin wajen kwamitin koli na JKS, ta wayar tarho, wanda ya halarci taron manyan wakilai masu kula da harkokin tsaro na kasashen BRICS a birnin Johannesburg.

A cewar Wang Yi, bana shekarar BRICS ne, Sin na goyon bayan Afrika ta Kudu wajen cimma nasarar daukar bakuncin shirya taron shugabannin kasashen BRICS da za a gudana a wata mai zuwa, ana imanin cewa, taron zai karawa hadin gwiwar kasashen BRICS kuzari.

Wang Yi kuma ya jadadda cewa, Sin da Afrika ta Kudu aminai ne, kuma ‘yan uwa. Sin za ta tsaya tare da Afrika ta Kudu duk da sauyawar yanayin duniya da ake fuskanta, da ma ingiza farfadowar kasar cikin hanzari, da mara wa Afirka ta Kudu baya wajen kara taka rawar a yankuna da ma duniya.

A nasa bangare, Ramaphosa ya ce, Afirka ta Kudu ta dora babban muhimmanci kan huldar bangarorin biyu, yana mai fatan kara hadin kansu a fannoni daban-daban. Afrika ta Kudu a shirye take don tabbatar da gudanar da taron kolin BRICS cikin nasara. Kasarsa kuma na fatan amfani da zarafi mai kyau don ingiza huldar kasashen biyu da huldar Afirka da Sin zuwa wani sabon matsayi.

Lokacin ziyararsa a Afirka ta Kudu, Wang Yi ya yi ganawa tare da ministar harkokin wajen kasar Grace Naledi Mandisa Pandor. (Amina Xu)