logo

HAUSA

Ana samu ingantuwar yanayin yi wa jama’a riga kafi a Afrika bayan annobar COVID-19

2023-07-26 10:50:51 CMG Hausa

 

Kawancen kasashen duniya kan samar da riga kafi wato GAVI, ya ce sannu a hankali, ana samun ingantuwar yanayin yi wa jama’a riga kafin cututtuka masu yaduwa duk da tsaikon da aka samu saboda mummunan tasirin annobar COVID-19.

Daraktan kula da harkokin sadarwa na GAVI Olly Cann, ya ce samun ingantuwar yanayin ya farfado da yakin da ake da cututtuka masu yaduwa a Afrika, ciki har da zazzabin cizon sauro da tarin jarirai da zazzabin Typhoid da cutar kwalara.

A cewar Olly Cann, an fi ganin ingantuwar yanayin yi wa jama’a riga kafi ne a kananan kasashe kamar Niger da Rwanda da Tanzania yayin da a kasashe kamar Nijeriya da Habasha da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, wadanda ke da fadi da yawan al’umma, suka ci gaba da kasancewa kan matakin da suke kai na yi wa jama’a riga kafi. (Fa’iza Mustapha)