logo

HAUSA

Shugaban kasa Mohamed Bazoum ya kaddamar da bikin fara ayyukan gina hanyoyi da birnin Yamai

2023-07-26 10:43:22 CMG Hausa

A ranar jiya ce Talata 25 ga watan Julin shekarar 2023, shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya jagoranci bikin kaddamar da katafaren aikin gina hanyoyi na matakin farko na shirin gyaran birnin Yamai, bisa hanyar route filingue da ke babban birnin Nijar.

Daga birnin Yamai, waikilinmu Mamane Ada ya turo mana da wannan rahoto. 

 

Su dai wadannan ayyuka sun kasance wasu sababbin ayyuka sake gina hanyoyi da bada kulawa gare su, da kuma tsawonsu ya kai kilomita 60, wadannan ayyuka za su lakumewa kudin sefa miliyar 50.8 wadanda bankin ci gaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika cewa da BOAD ya zuba, da kuma gwamnatin Nijar, in ji Moctar Gado Sabo, ministan kayayyaki da gine-ginen kasar Nijar.

Haka kuma shi wannan katafaren aiki ya kunshi gina hanyar RN1 da za ta tashi daga shataletale filin jirgin sama zuwa tashar biyan hanyar Yamai da Dosso.

Hanyar RN25 daga shataletalen Telwa zuwa fitar hanyar Filingue.

Hanyar Yamai-Nyala da za ta tashi daga shataletalen CEG 25 zuwa magangamar hanyar Tanimoun.

Da kuma hanyar Gamkale zuwa shimfidar gabar kogin Isa.

A cewar fadar shugaban kasa, wadannan ayyuka da za’a fara na daya daga cikin manyan alkawuran da shugaban kasa Mohamed Bazoum ya yi wa ’yan Nijar, musamman ma mazauna babban birnin Yamai. Haka kuma a cewar hukumomin Nijar, wadannan ayyuka, zaran an kammala su, birnin Yamai zai kasance cikin jerin manyan biranen nahiyar Afrika da ke samun bunkasuwa da kuma kyautatuwar jin dadin al’ummar birnin Yamai ta fuskar tsarin ci gaban birane da shugaba Mohamed Bazoum ya sa gaba.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai na jamhuriyar Nijar.