logo

HAUSA

An killace fadar shugaban kasar Nijar

2023-07-26 21:02:48 CMG Hausa

Wata majiya daga fadar shugaban kasar Nijar, ta bayyana a yau Laraba cewa, jami'an tsaron fadar shugaban kasar sun kange fadar shugaban kasar na wani dan lokaci, tun daga karfe 10:00 na daren jiya Talata bisa agogon kasar. Sai dai kawo yanzu babu wani ma’aikaci, ciki har da shugaban kasar Mohamed Bazoum da ya shiga ko ya fita daga fadar.

Yayin wata zantawa ta wayar tarho da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, wani jami'in ma'aikatar tsaron kasar ya bayyana cewa, shugaba Bazoum ya riga ya tattauna da wasu 'yan jam'iyyarsa, inda ya ce " nan ba da jimawa ba za a dawo da 'yanci". (Mai fassara: Bilkisu Xin)