logo

HAUSA

MDD: A kalla ma'aikatan agaji 18 ne suka mutu daga cikin dubban fararen hula da aka kashe a Sudan

2023-07-26 10:49:34 CMG Hausa

A jiya Talata ne mataimakin kakakin MDD ya bayyana cewa, a wani kira da aka yi na a ceci fararen hula, mai kula da ayyukan jin kai na MDD a kasar Sudan ta ba da rahoton cewa, an kashe ma'aikatan agaji 18 a cikin kwanaki 100 na rikicin.

Farhan Haq, mataimakin kakakin babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce sama da jami'an jin kai fiye da ashirin ne ake tsare da su, wasu kuma har yanzu ba a san inda suke ba. A kalla an wawushe ma’ajiyar kayayyakin jin kai 50, an kuma tarwatsa ofisoshi sama da 80, da sace motoci sama da 200.

"Jami'an kula da ayyukan jin kai sun yi kakkausar suka ga wadannan hare-hare, wadanda ke ci gaba da zama kalubale ga kokarin da muke yi na isar da muhimman kayan agaji ga mabukata," in ji Farhan.

“Ta tunatar da dukkan bangarorin dake rikici da juna a Sudan game da wajibcin da ya rataya a wuyansu a karkashin dokokin kare hakkin bil adama na kasa da kasa.” (Yahaya Babs)