logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu sakamakon gobarar daji a Aljeriya ya kai 34

2023-07-25 10:57:05 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Aljeriya ta sanar a ranar Litinin cewa, adadin wadanda suka mutu sakamakon gobarar daji a arewacin kasar Algeria ya karu zuwa 34, ciki har da sojoji 10.

Ma'aikatar ta ce kimanin mutane 8,000 ne ke yaki da gobarar a larduna 11, da manyan motoci 529 da kuma jirage masu saukar ungulu na kashe gobara da dama.

Gobarar ta tashi ne da daddare a ranar Lahadi musamman a lardunan Bejaia, Jijel, da Bouira, amma cikin sauri ta bazu saboda iska mai karfin gaske, inda ta yi barna sosai. (Yahaya Babs)