logo

HAUSA

Wang Yi: Intanet ba sabon fagen yaki ba ne

2023-07-25 09:29:16 CMG Hausa

Darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) Wang Yi, ya bayyana cewa, babbar manufar intanet ita ce bude kofa, kuma hanyar sadarwa ba wani sabon fagen yaki ta mallakar fasahar ba ce.

Wang, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya bayyana haka ne jiya Litinin, yayin wani taro a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu. Ya bayyana karara cewa, kasar Sin tana adawa da duk wani nau'in na nuna danniya a fannin wata fasaha ko harkar intanet.

Haka kuma, ya yi kira da a kara tattaunawa tare da samar da kyakkyawar alkiblar hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS. Ya kuma ce ya kamata tsarin amfani da intanet ya kasance bisa adalci, a bude ga kowa ba kuma tare da wata matsala ba.

Wang ya kara da cewa, ana martaba tsaron intanet a kasar Sin, yana mai cewa, kasar Sin tana son inganta sadarwa da hadin gwiwa da dukkan kasashe masu tasowa, da ma kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa, da sa kaimi ga ciyar da tsarin tafiyar da harkokin intanet a duniya gaba. (Ibrahim)