logo

HAUSA

Liu Jianchao ya ziyarci kasar Mauritius

2023-07-25 20:51:23 CMG Hausa

Shugaban sashen kula da harkokin tuntubar kasashen waje, na kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) Liu Jianchao, ya jagoranci tawagar ‘yan JKS, zuwa kasar Mauritius, inda suka gudanar da ziyarar aiki, tare da ganawa da shugabannin manyan jam'iyyun siyasar kasar. Liu da tawagar sa, sun ziyarci Mauritius din ne tsakanin ranaikun Asabar zuwa Talatar nan.

A yayin ganawar sassan biyu, jami’an sun yi imanin cewa, ya zama wajibi a aiwatar da muhimmin ra'ayin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da nuna amincewar juna ta fuskar siyasa, da samun moriyar juna a fannin tattalin arziki, da sada zumunci tsakanin jama'a, don karfafa mu'amala tsakanin jam'iyyu, da inganta hadin gwiwa ta fuskokin tattalin arziki da cinikayya, da al'adu da ilimi, da samar da ababen more rayuwa, da sauyin yanayi, da dai sauransu, da yaukaka dankon zumunci tsakanin jama'a, da taimakawa ciyar da dangantakar dake tsakanin Sin da Mauritius, da ta Sin da Afirka gaba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)