logo

HAUSA

Al’ummar kauyen garin Bako ta jihar Gombe sun nemi daukin ababen more rayuwa

2023-07-25 09:40:06 CMG Hausa

Al’ummar kauyen garin Bako dake cikin yankin gundumar Kamu a karamar hukumar Kaltingo dake jihar Gombe a arewa maso gabashin Najeriya sun koka ainun kan matsalolin rashin ababen more rayuwa musamman ruwan sha da asibiti da kuma hanyar mota.

A lokacin da suke zagayawa da wani ayarin manema labarai sassan kauyen, al’umomin sun ce duk da yawan da suke da shi har yanzu asibiti daya ne a garin wanda yake da gadon kwanciya guda daya, sannan kuma ga matsalar rafi daya ke hana su jigilar kayan amfani gona zuwa kasuwanni.

Daga tarayyar Najeriya Wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Kauyen garin Bako dake kudancin jihar ta Gombe yana da tazarar kilomita 85 ne tsakaninsa da fadar gwamnatin jihar, al’umomin yankin kuma sun ce sun dauki lokaci suna gabatar da korafin su ga mahukunta domin kawo musu dauki amma abun ya faskara.

Malam Abdullahi mai caji yana daya daga cikin mazauna wannan kauyen.

“Mun tsinci kanmu cikin kunchi na rayuwa matsalar ruwa, asibiti, makaranta, sannan kuma babbar matsalar ita ce kogin dake yankin inda a duk lokacin da aka yi ruwan sama ba ma iya fita zuwa ko ina , ko da mara lafiya ka dauko haka za ka hakura har ya rasa ransa.”

A lokacin da ake jinta bakinsa kan wanann korafi, babban daraktan yada labaran gwamnan jihar Gombe Alhaji Isma’ila Uba Misli ya ce, gwamnati na bakin kokarin ta wajen kyautata yanayin rayuwar mazauna karkara.

“A cikin gundumomi 114 dake jihar Gombe babu wata gunduma guda daya da gwamnan jihar bai yi kokarin kai musu asibiti ba ko kuma ya gyara musu asibitin da yake wurin ba domin moriyar al’ummar yankunan, a sabo da haka wannan kadai ya nuna cewa ko ina za a iya zuwa a yi musu ayyukan muddin dai suka yi hakuri.”

Daraktan yada labaran gwamna na jihar Gombe ya ci gaba da cewa gwamnati na sane da matsalolin da al’ummar kauyen ke fuskanta musamman batun asibiti da ruwan sha da kuma rafin dake  barazana ga rayuwar mazauna yankin a duk lokacin damuna, kuma bada jimawa ba za a kai musu dauki. (Garba Abdullahi Bagwai)