logo

HAUSA

Likitocin kasar Sin za su taimaka wajen yaki da cutar sankarar bakin mahaifa

2023-07-25 10:35:27 CMG Hausa

Wata tawagar likitocin kasar Sin ta sauka a Freetown, babban birnin kasar Saliyo a jiya Litinin, domin taimakawa kasar yaki da cutar sankarar bakin mahaifa.

Ana sa ran likitoci wadanda suka fito daga asibitin kula da mata da kananan yara na lardin Hunan, za su shafe sama da makonni biyu a kasar, inda za su taimaka tare da horar da jami’an kasar kan kyautata kulawa da marasa lafiya, ta hanyar gabatar da kwarewarsu a fannonin bincike da kula da gano cutar ta sankarar bakin mahaifa.

Yayin liyafar tarbar likitocin a jiya, shugabar asusun kula da yawan al’umma na MDD a kasar Nadia Rasheed, ta ce sankarar bakin mahaifa ita ce cuta ta biyu mafi sabbaba kisan mata a Saliyo, inda yake haifar da matsananciyar wahala da asarar rayuka.

Jami’ar ta kuma yabawa likitocin Sinawa bisa wannan kyakkyawan yunkuri, tana mai cewa, suna matukar farin ciki da ziyararsu a kasar domin gabatar da ilimi da kwarewarsu da kuma bayar da horo. (Fa’iza Mustapha)