logo

HAUSA

Jami`ar Bayero ta fitar da matakan rage radadin cire tallafin mai ga ma`aikata

2023-07-24 10:36:59 CMG HAUSA

 

Sama da ma’aikata 2,000 dake jami’ar Bayero ta Kano a arewacin Najeriya za su amfana da tallafin rage radadin da cire tallafin man fetur zai haifar ga yanayin rayuwarsu.

Shugaban jami’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas ne ya tabbatar da hakan jiya Lahadi yayin babban taron masu ruwa da tsaki na jami’ar karo na 56 wanda aka gudanar a babban dakin bikin yaye dalibai dake sabuwar harabar jami’ar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.