logo

HAUSA

Wani soja ya kashe fararen hula a kalla 13 a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

2023-07-24 09:41:24 CMG Hausa

Rundunar sojin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ta ce daga ranar Asabar zuwa jiya Lahadi, wani sojan rundunar ya kashe fararen hula a kalla 13, a wani kauyen yankin Nyamamba dake lardin Ituri na gabashin kasar.

Jules Ngongo, kakakin rundunar sojin lardin Ituri, ya ce a kalla yara 10 na daga cikin wadanda sojan ya kashe. Ya kara da cewa, galibin wadanda lamarin ya rutsa da su ‘yan uwan sojan da ya yi harbe harben ne, yana mai cewa, rikicin iyali ne musababbin aukuwar lamarin.

Tuni dai hukumomin soji suka kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan kasha kashen. (Fa’iza Mustapha)