logo

HAUSA

Sojojin Sudan: Mutane 9 ne suka mutu a hatsarin jirgin sama a filin jirgin saman Port Sudan

2023-07-24 10:17:18 CMG Hausa

A kalla mutane 9 ne suka mutu a ranar Lahadi a wani hadarin jirgin sama na farar hula a filin jirgin saman Port Sudan da ke gabashin jihar Bahar Maliyar kasar, in ji rundunar sojojin kasar Sudan.

Sanarwar da ofishin kakakin rundunar sojin Sudan ya fitar ta ce, hatsarin da wani jirgin Antonov ya yi da maraice a filin tashi da saukar jiragen saman ya faru ne saboda "matsalar da jirgin ya samu."

Mutanen tara da suka mutu sun hada da sojoji hudu, amma wata yarinya ta tsira daga hadarin, a cewar sanarwar.

Filin jirgin saman Port Sudan mai nisan kilomita 890 gabas da birnin Khartoum, ana amfani da shi a matsayin babban filin jirgin saman kasar bayan da filin jirgin saman Khartoum ya daina aiki saboda arangama tsakanin bangarorin sojojin kasar. (Yahaya)