logo

HAUSA

A kalla mutane 16 sun mutu sakamkon ruftawar wani gini a Kamaru

2023-07-24 09:55:41 CMG HAUSA

 

Gwamnan lardin Littoral dake kasar Kamaru, Samuel Dieudonne Ivanaha Diboua ya bayyana cewa,   mutane 16 ne suka mutu, yayin da fiye da 20 suka jikkata, bayan da wani gini mai hawa 4 ya rufta da sanyin safiyar jiya a Doula, cibiyar kasuwancin kasar Kamaru

Diboua ya ce, akwai yara da mata a cikin wadanda lamarin ya shafa. Yana mai cewa, masu aikin ceto na ci gaba da neman mutanen da suka bace a karkashin baraguzan ginin.

Ya shaidawa manema labarai a lokacin da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru cewa, sojoji da ma’aikatan kashe gobara, da ’yan sanda, da dukkan jami'an tsaro na gudanar da aikin ceto.

A cewar masana na cikin gida, an sha samun rushewar gine-gine a birnin, sanadiyar ambaliyar ruwa, da rashin bin tsare-tsare da ka'idoji na gine-gine, da kuma amfani da kayayyaki marasa inganci yayin gini. (Ibrahim Yaya)