logo

HAUSA

Sama da wakilai 1200 ne za su halarci taron saka jari na shugabannin kasashen Afirka a Tanzaniya

2023-07-24 12:20:26 CMG HAUSA

 

A kalla wakilai 1200 ne, ake saran za su halarci taron shugabannin Afirka kan saka jari, da za a yi a daga ranakun 25 da 26 ga watan Yuli a birnin Dar es Salaam mai tashar jiragen ruwa na Tanzaniya.

Kwamishinan yankin Dar es Salaam, Albert Chalamila ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, wakilan da suka hada da shugabannin kasashe, za su fito ne daga kasashen Afirka fiye da 30.

Chalanba ya bayyana cewa, Dar es Salaam ya kimtsa karbar wakilai wadanda kuma za su samu damar more dimbin wuraren yawon bude ido da Allah ya horewa kasar.

A ranar 19 ga watan Mayu ne, shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta kaddamar da shirye-shiryen gudanar da taron, inda ta yi kira ga sauran shugabannin kasashen Afirka, da masu tsara manufofi, da sauran masu ruwa da tsaki a fannin raya kasa, da su kara zuba jari a fannonin koyo, da kiwon lafiya, da sana'o'i don tabbatar da albarkar al'ummar dake akwai a yankin a matsayin babbar kadara.

Taron wanda bankin duniya ke daukar nauyi, zai gudana ne a karkashin taken "hanzarta ci gaban tattalin arzikin Afirka: Bunkasa Matasa ta hanyar inganta koyo da kwarewa."

Ana sa ran taron zai hallara shugabanni daga ko’ina a nahiyar Afirka, don mai da hankali tare da zayyana alkawurran kudi da manufofi a zahiri da ke ba da fifikon saka hannun jari a bangaren mutane a matsayin ginshikin inganta samar da kayayyaki, juriya, da ci gaba. (Ibrahim).