logo

HAUSA

UN: Najeriya tana da karfin samar da wadataccen abinci da kanta

2023-07-23 16:08:46 CMG Hausa

Majalissar dinkin duniya ta tabbatar da cewa Najeriya tana da dukkan damarmakin da za ta wadata al’ummar kasa da abinci ba tare da odarsa daga wasu kasashen ketare ba, duk kuwa da kalubalen da ake fuskanta a bangarorin ci gaban kasar.

Babban jami’in ayyukan jin kai na Majalissar a Najeriya Mr. Matthias Schmale ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Abuja a karshen mako a game da shirye-shiryen babban taron koli kan tasirin zamantakewar Afrika da za a gudanar a birnin Legas a watan gobe.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Babban jami’in majalissar dinkin duniyar ya ce, domin cimma wannan hasashe da aka yi, wajibi ne mahukunta a Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki a fannin sha’anin aikin gona su hada kai wajen fito da tsarin mai dorewa da zai dora kasar kan turbar zamani na aikin gona.

Ya ce yunkurin gwamnatin kasar na kwanan nan da shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya yi na yakar yunwa a kasar ta hanyar samar da wadataccen abinci zai taimaka matuka wajen samuwar jari mai ma’ana a bangaren, wanda hakan kuma zai shawo kan jerin kalubale da kasar ta dade tana cin karo da su.

Mr Schmale wanda ya tabbatar da cewa karfin arzikin Najeriya ta fuskar ma’adanai da kasar noma zai iya sanyawa ta ci da kanta, amma dole ne sai mayar da hankali kan tsarin aikin noma mai dorewa.

Ya ce sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi a kasar wanda ya haifar da hauhawar farashin kayayan abinci, wakilin majalissar dinkin duniyar a Najeriya ya jaddada aniyar majalissar na taimakawa kasar wajen tsara matakan rage radadi ga ’yan kasar, haka kuma majalissar za ta yi aiki tare da gwamnatin tarayyar Najeriya wajen assasa dabaru masu dorewa da za su tabbatar da ingantuwar noma da kuma dakile tasirin sauye-sauyen tattalin arziki. (Garba Abdullahi Bagwai)