logo

HAUSA

Shugaban Kasar Kenya Ya Gana Da Wang Yi

2023-07-22 21:54:13 CMG Hausa

Shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto, ya gana da daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) , kana mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar, Wang Yi, a birnin Nairobi na kasar Kenya, a yau Asabar. Inda bangaorin 2 suka bayyana niyyar raya huldar dake tsakanin kasashen 2 zuwa wani sabon mataki. (Bello Wang)