logo

HAUSA

Annobar cutar numfashi ya yi sanadiyar rufe wasu makarantun firamare da na sakandire a jihar Kaduna

2023-07-22 14:40:54 CMG HAUSA

 

Gwamnatin jihar Kaduna dake arewacin Najeriya ta bayar da umarnin rufe makarantun firamare da na sakandire a yankin Kafanchan dake karamar hukumar Jema’a sakamakon barkewar cutar dake haifar da matsalar numfashi.

An samu rahoton barkewar cutar jiya Juma’a wadda ta yi sanadin mutuwar a kalla mutane 10, yayin da wasu kuma ke kwance a asibiti.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.