logo

HAUSA

Liu Jianchao ya kai ziyara Madagascar

2023-07-22 21:40:53 CMG HAUSA

Shugaban sashen hulda da kasashen waje na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Liu Jianchao, ya jagoranci wata tawagar JKS don kai ziyarar aiki a Madagascar daga ran 20 zuwa 22, inda ya gana tare da yin musayar ra'ayi da shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina da sauran manyan jami'an gwamnati da na jam'iyyun siyasa. Bangarorin biyu sun amince cewa, wajibi ne a kara mu’ammalar jam’iyyu da hukumomin kafa dokoki da al’umma tsakaninsu, ta yadda za a ingiza huldar kasashen biyu zuwa wani sabon mataki. (Amina Xu)