logo

HAUSA

Sin da Afirka sun yi alkawarin karfafa hadin gwiwar soja a tsakaninsu

2023-07-22 21:34:52 CMG Hausa

Kasashen Sin da nahiyar Afirka, karkashin laimar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) sun lashi takwabin karfafa hadin gwiwar soja da aka riga aka cimma, ta yadda sassan biyu za su cimma burinsu na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka da ma ragowar sassan duniya.

Wannan na zuwa ne a yayin liyafar bikin cika shekaru 96 da kafuwar rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin da aka gudanar a yammacin jiya a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Taron ya hallara wakilan sojoji na kasashen Afirka daban-daban, da manyan jami'an gwamnatin Habasha, da wakilan jami'an diplomasiyya na kasar Habasha, gami da wakilan jama'ar kasar Sin dake kasar Habasha.

A yayin bikin, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Sin a kungiyar AU, Guo Baojian ya bayyana cewa, idan har babu tsaro da kwanciyar hankali, to, ba za a samu ci gaba ba. (Ibrahim)