logo

HAUSA

Sin da Habasha sun amince su inganta hadin gwiwa da ma alakar Sin da Afirka

2023-07-22 15:45:43 CMG Hausa

Firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya gana da daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) Wang Yi jiya Jumma’a, inda bangarorin biyu suka yi alkawarin inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Wang, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya kai ziyara kasar Habasha ne, a kan hanyarsa ta hakartar taron masu ba da shawara kan harkokin tsaron kasa na kasashen BRICS karo na 13, da zai gudana a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.

A yayin ganawarsa da Wang, Abiy Ahmed ya yi karin haske kan manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma, yayin da take bin tafarkin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, yana mai cewa, ya yaba da yadda kasar Sin take nacewa kan tafarkin ci gaba da ya dace da yanayin kasarta, gami da saurin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewa da ta samu, wanda ya zama abin koyi ga ragowar kasashe masu tasowa.

A nasa bangaren kuwa, Wang Yi ya bayyana cewa, Habasha babbar kasa ce a nahiyar Afirka da ke da tasiri mai mahimmanci. Yana mai cewa a matsayinsu na abokan huldar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, Sin da Habasha suna da buri daya, kuma sun gudanar da hadin gwiwa mai inganci bisa tsare-tsare irin su "shawarar ziri daya da hanya daya" da dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka, wanda ke jagorantar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka.(Ibrahim)