logo

HAUSA

Sin da Habasha sun sha alwashin inganta zaman lafiya da ci gaba a yankin kahon Afirka

2023-07-22 15:22:31 CMG Hausa

Darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS Wang Yi, ya gana da mataimakin firaministan kasar Habasha kuma ministan harkokin wajen kasar Demeke Mekonnen.

Yayin ganawar, Wang ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kasar Habasha wajen kiyaye ikonta mulkin da cikakkun yankunanta, da goyon bayan kasar wajen cika alkawarin da ta dauka na tabbatar da hadin kai da zaman lafiyar kasar, tana kuma goyon bayanta wajen taka muhimmiyar rawa a harkokin shiyya-shiyya da na kasa da kasa.

Ya kara da cewa, Sin na son yin aiki tare da Habasha wajen aiwatar da manufar zaman lafiya da ci gaba a yankin kahon Afirka, da tallafa wa jama'ar Afirka wajen warware matsalolin Afirka ta hanyar da ta dace da Afirka.

A nasa bangaren, Mekonnen ya bayyana cewa, kasar Habasha tana da dadadden tarihi wajen raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma tana da niyyar karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin a matakan kasashen biyu, da shiyya-shiyya da kuma sassa daban-daban.

Ya ce, Habasha ta yaba da irin taimakon da kasar Sin take ba ta, wajen kiyaye tsaro da zaman lafiyarta, tana kuma fatan kasar Sin za ta kara taimaka mata wajen tabbatar da zaman lafiya, da aiwatar da gyare-gyare, da ma farfado da tattalin arzikinta yadda ya kamata. (Ibrahim)