logo

HAUSA

Najeriya ta kaddamar da shirin rabon tallafin alluran riga-kafin cutar Covid-19

2023-07-21 09:52:28 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya sun kaddamar da shirin rabon tallafin alluran riga-kafin cutar Covid-19 na tsabar kudi har fiye da dalar Amurka miliyan 9.26 domin rabawa ga wasu jihohin kasar. 

Tallafin na tsawon shekaru biyu da kasar Canada ta bayar da gudummawa ta hannun hukumar lafiya ta duniya da zummar isarwa ga mutane da yankunan da suke cikin hadarin kamuwar da cutar, a wani mataki na karfafa sha’anin kiwon lafiya a kasar baki daya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A lokacin da yake jawabi yayin bikin kaddamar da shirin rabon alluran,wakilin hukumar lafiya ta duniya a Najeriya Mr Walter Kazadi-Mulombo cewa ya yi, tallafin zai baiwa ofishin hukumar damar bayar da tallafin fasaha don karfafa tsarin kiwon lafiya musamman sarrafa bayanai da sa ido a kan tsare-tsaren kiwon lafiya a kasashen dake nahiyar Afrika.

Daga bisani a nasa jawabin, babban darakta na hukumar lafiya matakin farko ta tarayyar Najeriya Dr. Faisal Shu’aib, ya ce kaso 70 na adadin ’yan Najeriya sun amfana da allurar riga-kafin Covid-19 guda daya tun bayan da aka kaddamar da shirin a cikin watan Maris na shekara ta 2021

Ya ce za a yi amfani da tallafin kasar ta Canada ne ga jahohin da ba su taka rawar a zo a gani ba wajen riga-kafin cutar.

Jihohin kuwa kamar yadda ya fada sun hada da Ondo, da Rivers, da Kogi, da Delta, da Ebonyi, da Legos da Akwa-Ibom.

Sauran su ne Bayelsa, Benue, Ogun, Katsina, Taraba, Anambra, Kebbi da kuma jihar Edo. (Garba Abdullahi Bagwai)