logo

HAUSA

Masana : Darussa daga shirin kawar da talauci na kasar Sin na da muhimmanci ga Afrika

2023-07-21 12:35:06 CMG Hausa

A ranar Laraba a wani taron karawa juna sani da aka gudanar ta kafar bidiyo, masana da jami’ai sun bayyana cewa, kasashen Afirka za su iya koyon darasi daga nasarar yaki da fatara ta kasar Sin don ciyar da kasashen gaba.

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Rwanda da shirin nazarin Afirka da Sin suka shirya taron na karawa juna sani kan kawar da fatara. Nasarar da kasar Sin ta samu ta zaburar da kasashen Afirka dake kokarin samun ci gaba mai dorewa, in ji kwararrun a wajen taron.

Zeno Mutimura, jami'in diflomasiyyar Rwanda dake magana a matsayin babban bako a taron, ya ce Afirka za ta iya koyi da kasar Sin don rage talauci a nahiyar, kamar tabbatar da "manufofin da suka shafi jama'a."  Ya ce kasar Rwanda ta fitar da mutane miliyan daya daga kangin talauci ta hanyar ayyuka irin na kasar Sin da suka mayar da hankali kan gina jama'a.

Mweusi Karake, tsohon jami'i a kasuwar gamayya ta Gabas da Kudancin Afirka, ya ce kasar Sin ta yi nasarar rage talauci a kasarta ne ta hanyar yin la’akari da yanayin zamantekewar al’ummarta da bukatunsu. Ya ce "Babban matsalar Afirka ita koyi da kasashen yammacin duniya ba tare da tunani ba... a gano abin da zai amfanar da jama’a kafin a yi koyi da shi,” in ji Mweusi Karake. (Yahaya Babs)