logo

HAUSA

Shugaban kasar Nijar ya baiwa jami’an tsaro na FDS kwarin gwiwa da ke yankin Tahoua

2023-07-21 09:14:24 CMG Hausa

Cikin tsarin rangadin aiki da ya fara a ranar Laraba 19 ga watan Yulin shekarar 2023 a yankin Tahoua, shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum tun saukarsa a yankin Ader, ya kai ziyara sansanin jirage masu sarrafa kansu na rundunar sojojin sama, kafin ya ziyarci sansanin soja na 42 BIA na shiyyar tsaro mai lamba 4, domin baiwa sojoji kwarin gwiwa gaban kalubalen tsaro da suke fuskanta.

Daga birnin Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum da farko ya jinjinawa jami’an tsaro na FDS dake yankin Tahoua kafin ya ba su kwarin gwiwa nasu ci gaba cikin wannan kwazo da daukar niyya da kuma nacewa gaban kalubalen tsaro. Wannan shiyyar, a cewar shugaban kasa, kuma shugaban rundunar sojojin Nijar, shiyya ce dake da muhimmanci sosai wajen tsaron fadin kasar Nijar.

Ga jaruman jami’an tsaro na FDS, shugaban kasar Nijar ya ce, domin kuna nan ne, kuke nacewa kai da fata cikin aikinku, kuma kuke haskawa nesa daga sansanoninku na asili, cikin yanayi mai matukar wahala na wannan matsala da ta bambanta da saura, domin ’yan Nijar su kwana lafiya su tashi lafiya.

Mai iyaka da Aljeriya, Najeriya da Mali, kasar Nijar tana fama da hare-hare da dama daga kungiyoyin ta’addanci, musamman ma wadanda suke kai hare-hare a arewacin Mali da kuma Boko Haram cikin yankin tafkin Chadi.

Duk da girman barazanar, jaruman sojojinmu sun nuna kamar yadda suka saba, rashin tausayi gaban wadannan tsirarrun ’yan ta’adda da suke yada tsoro da tashin hankali cikin al’umomin wadannan yankuna.

Dalilin ke nan, shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum bai yi kasa a gwiwa ba domin tabbatarwa sojoji cewa za’a ba su dukkan halin da ya dace domin su tafiyar da aikinsu na kishin kasa.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.