logo

HAUSA

Shugaban Nijar ya halarci bikin kaddamar da kamfanin siminti da kamfanin Sin ya zuba jari da gina

2023-07-20 19:00:38 CMG Hausa

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazum ya halarci bikin bude da kamfanin siminti jiya Laraba, wanda wani kamfanin kasar Sin ya zuba jari da kuma gina shi.

A jawabinsa yayin bikin, shugaba Bazum ya gode wa kasar Sin bisa goyon bayan da ta dade tana baiwa Nijar, yana mai jaddada cewa, masana'antar ta kara inganta matsayin Nijar wajen raya masana'antu, wanda ya sanya shi zama wani abin koyi na hadin gwiwa mai inganci tsakanin Nijar da Sin.

A nasa jawabin, jakadan kasar Sin a jamhuriyar Nijar Jiang Feng ya bayyana cewa, nasarar kaddamar da kamfanin simintin, zai mayar da Jamhuriyar Nijar daga mai shigo da siminti zuwa kasa mai fitar da siminti. Yana mai cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta kara karfafa hadin gwiwar zuba jari a tsakanin sassan biyu, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a zahiri a tsakanin kasashen biyu, don samar da karin sakamako.

Kamfanin simintin dai yana garin Illela na yankin Tahoua a kasar ta Nijar, inda ake fitar da siminti tan miliyan 1.5 duk shekara. (Ibrahim)