logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bukaci samun ci gaba tare gami da makomar bai daya ga daukacin bil Adama

2023-07-20 20:20:58 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya jaddada muhimmancin hada karfi da karfe wajen samun ci gaba tare wajen samun kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil Adama.

Zhang ya bayyana haka ne a babban taron muhawarar manyan jami'an siyasa kan ci gaba mai dorewa, wanda aka fara daga ranar Litinin zuwa Laraba, yana mai cewa, wajibi ne mu sanya ci gaba da gaske a cikin ajandar raya kasashe. Dole ne a tattara dukkan albarkatu don samar da haɗin gwiwa mai karfi, ta yadda za a tabbatar da cewa, kowa ya darajanta ci gaba kuma dukkan kasashe suna yin hadin gwiwa tare. Idan kuma ana son tabbatar da manufofin maradun ci gaba mai dorewa na MDD wato SDGs, bai kamata a bar wani ko wata kasa a baya ba. (Ibrahim)