logo

HAUSA

An yaba da hadin kan dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin a ayyukan jin kai na MDD

2023-07-20 10:37:14 CMG Hausa

A ranar Talata ne wakiliyar musamman ta babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Bintou Keita ta yaba da hadin kan da sojojin wanzar da zaman lafiya na kasar Sin suka nuna wajen gudanar da ayyukan jin kai a yankin gabashin kasar.

Ta yi wadannan kalamai ne a wajen bikin kaddamar da wata gada ta wucin gadi da ta ratsa kogin Luzira a yankin Kalehe na lardin Kivu ta Kudu, yankin da ruwan sama mai karfi da ambaliya a watan Mayu ya yi kamari, wanda ya janyo hasarar rayuka.

Gadar mai muhimmanci ga jigilar kayayyakin jin kai da zirga-zirgar jama'ar yankin, injiniyoyin dakaru na 26 na kasar Sin ne suka gina ta, bisa umarnin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo (MONUSCO).

Yayin da take taya murnar nasarar da aka samu a wannan aikin jin kai, Keita, shugabar kungiyar MONUSCO, ta yaba musamman, da hadin kan da dakarun Sin masu shudin hula suka nuna. (Yahaya)