logo

HAUSA

Kremlin: Putin zai halarci taron BRICS ta hanyar kafar bidiyo

2023-07-20 11:53:34 CMG Hausa

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya bayyana a jiya Laraba cewa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai halarci taron kasashen BRICS da za a yi, ta hanyar kafar bidiyo, inda ya kara da cewa, shugaban na Rasha na da niyyar halartar taron baki daya.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ne zai halarci taron a zahiri, in ji Peskov.

Za a gudanar da taron koli na BRICS karo na 15 mai taken "BRICS da Afirka: Hadin kai don hanzarta ci gaban juna, da ci gaba mai dorewa da jin ra’ayin jama'a" a birnin Johannesburg daga ranar 22 zuwa 24 ga watan Agusta. (Yahaya Babs)