logo

HAUSA

UNICEF: Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a yaki da cututtuka masu saurin halaka kananan yara

2023-07-20 10:27:52 CMG Hausa

Hukumar lura da kananan yara ta majalissar dinkin duniya UNICEF ta aiyana Najeriya a matsayin kasashen da suka samu gagarumar nasara wajen gudanar da allurar riga-kafin cututtukan nan 6 masu saurin halaka kananan yara.

Babban jami’in hukumar dake kula da shiyyar Kano Mr. Rahama Farah ne ya tabbatar da hakan jiya Laraba 19 ga wata a birnin Kano yayin taron wayar da kai na tsawon yini biyu da aka shirya wa manema labarai.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

An dai shirya taron ne bisa tsarin hadin gwiwa da hukumar wayar da kan jama’a ta tarayyar Najeriya da kuma hukumar ta Unicef, an shirya shi hususan domin neman hadin kan ’yan jaridu da sauran masu ruwa da tsaki wajen wayar da kan iyaye game da muhimmancin allurar riga-kafin.

Mr Rahama Farah ya ce duk da wadannan nasarori da Najeriya ta samu, amma dai har yanzu akwai gibi na sama da kananan yara 600,000 dake jihohi uku na arewacin Najeriya wadanda suka kunshi jihohin Kano, Jigawa da Katsina da ba a yiwa allurar riga kafin cututtukan dake sauran halaka kananan yaran ba.

Wannan adadi ya dauki kaso 40 na kananan yaran da aka yiwa allurar a Najeriya baki daya, inda ya kara da cewa daga cikin adadin sama da kananan yara 300,000 a jihar Kano suke lamarin da ya kai kaso 50 na jahohin uku.

Ya ce ya zama wajibi a kara daukar matakai domin dakile ci gaba da samun wannan gibi, kuma ’yan jaridu na da rawar da za su taka a wannan fage.

“Akwai kauyuka da jami’an lafiya ba sa iya zuwa sabo da rashin hanya mai kyau, sanann wasu al’umomin suna zaune ne a bayan duwatsu, akwai kuma wasu kauyukan da har yanzu mutane ba su amunta da allurar ba, ba sa bari a yiwa ’ya’yan su ko da kowa jami’an lafiya sun je garuruwansu, sai kuma wasu kauyukan da matsalar tsaro bata bari a kai gare su ana fuskantar masu garkuwa da mutane a wuraren wanda hakan yake razanar da jami’in lafiya zuwa wannan shi ya sanya aka samu adadin kananan yara har 600,000.”

Haka kuma Dr Shehu Mohammad ya ce labaran karya da na rudarwa a game da allurar da wasu kafofin labarai ke yadawa shi ma ya taimaka sosai wajen gaza samun amincewar iyayen yara a kan tasiri da muhimmancin riga-kafin ga dorewar lafiyar ’ya’yan su. (Garba Abdullahi Bagwai)