logo

HAUSA

Liu Jianchao ya halarci taron tattaunawar jam'iyyun siyasa na BRICS

2023-07-20 20:33:14 CMG Hausa

Daga ranar 17 zuwa 20 ga watan Yuli, Liu Jianchao, shugaban sashen hulda da kasashen waje na kwamitin kolin JKS, ya jagoranci tawagar JKS, don halartar taron tattaunawa na jam'iyyun siyasa na kasashen BRICS da kuma ziyarar Afirka ta Kudu, inda ya gana da shugaban majalisar wakilan jama'ar Afirka ta Kudu kuma shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, da sauran manyan jami'an kasar Afirka ta Kudu. Bangarorin biyu sun bayyana cewa, za su inganta mu'amalar jam'iyyu da karfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsaren bangarori da dama kamar BRICS.

A yayin bikin bude taron, Liu Jianchao ya gabatar da jawabi a gun taron jam'iyyun siyasa, inda ya jaddada cewa, ya kamata kasashen BRICS su karfafa hadin kai da hadin gwiwa, tare da sa kaimi ga ci gaban zaman lafiya da wayewar kan bil-Adama. (Ibrahim)