Yawan Mutane Shi Ne Kasuwa…
2023-07-20 20:58:32 CMG HAUSA
DAGA SAMINU ALHASSAN
Yayin da karin kasashen Afirka ke zurfafa cudanyar cinikayya da kasar Sin, masharhanta na kara bayyana kwarin gwiwa game da fatan shigar karin hajojin nahiyar Afirka cikin babbar kasuwar Sin. Musamman ma a wannan gaba da kamfanonin sassan biyu ke kara fadada alaka, da lalubo sabbin damammakin cin gajiya daga arzikin babbar kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Yanzu haka, katafariyar kasuwar Gaoqiao dake birnin Changsha, ta zamo babban sansanin baje hajojin albarkatun gona daga kasashen Afirka, tare da bazuwarsu zuwa dukkanin sassan kasar Sin. Ana iya cewa, hakan sakamako ne na managarcin tsarin cudanyar cinikayya tsakanin Sin da kasashen na Afirka, karkashin shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya”, da kuma manufofin bude kofa da Sin ke yi ga sauran sassan kasa da kasa. Baya ga tanade-tanaden dake kunshe cikin manufofin hadin gwiwar Sin da Afirka na dandalin FOCAC.
Daya daga cikin fannoni mafiya muhimmanci da kasashen Afirka ke cin kasuwar kasar Sin a baya bayan nan shi ne cinikayyar albarkatun gona, inda ko da a baya bayan nan ma manoman kasar Kenya, suka samu zarafi na shigar da nau’o’in furannin daban daban cikin wannan babbar kasuwa ta kasar Sin.
Wannan kari ne kan wasu nau’in mai da ake tatsa daga wasu tsirrai, wanda shi ma ake kawowa daga Madagascar, da gahawar kasar Habasha, wadanda dukkanin su ke samun karin kasuwa a Sin.
A halin da ake ciki, akwai karin kamfanonin Afirka dake kafa rassan su, tare da gudanar da hada-hadar cinikayya a kasuwar Gaoqiao dake birnin Changsha.
Ga karin manoman kasashen Afirka dake fatan shigar da albarkatun gona cikin kasuwannin kasar Sin, muna iya cewa dama ta samu, domin kuwa kasuwar kasar wadda ke kara fadada a halin yanzu tana da tagomashi, da yanayi mai kyau na bunkasa, wanda hakan zai baiwa manoman kasashen Afirka karin damammaki na samun alherai, bayan shafe tsawon lokaci suna dogaro kadai ga kasuwannin Turai da Amurka.