logo

HAUSA

Kasa Da Kasa Sun Yaba Da Jawabin Shugaba Xi Kan Kare Muhalli Da Halittu

2023-07-20 11:07:21 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar inganta gina kasar Sin mai kyan gani da gaggauta samun ci gaban zamanantarwa mai kunshe da zaman jituwa tsakanin bil Adama da muhalli.

Xi Jinping ya bayyana haka ne cikin muhimmin jawabin da ya gabatar yayin da ya halarci taron kasa kan kare muhalli da halittu, wanda ya gudana a birnin Beijing daga 17 zuwa 18 ga wata.

Jami’ai daga kasashe da dama sun yabawa jawabin, sun kuma yi imanin cewa, kasar Sin na ci gaba da gina tsarin wayewar kai ta fuskar muhalli ta yadda muhallin halittu zai amfanawa al’umma da duniya, kuma ta samu manya nasarori da suka ja hankalin al’ummar duniya. Sun kuma yi imanin cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bayar da muhimman gudunmuwa ga kyautata gina duniya da ma ci gaban duniya mai dorewa.

A jiya ne Solomom Lechesa Tsenoli, mataimakin shugabar majalisar dokokin Afrika ta Kudu, ya ce kasar Sin ta dauki muhimman matakai wajen kare halittu da muhallinsu, kuma matakan sun zama abun koyi ga sauran kasashe.

Shi kuwa Shevarnev, babban mai bincike a cibiyar nazarin shari’a da kwatanta tsarin shari’o’in kasa da kasa ta kasar Rasha cewa ya yi, cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta yi ta nuna misalin kasar da ta san ya kamata a tsakanin kasashen duniya kan batutuwan da suka shafi kare muhalli da halittu, musammam wajen amfani da makamashin da ake iya sabuntawa. Baya ga haka, gwamnatin Sin na mayar da hankali matuka wajen kare muhalli da halittu a yankunan kasar dake da karancin ci gaba. (Fa’iza Mustapha)