logo

HAUSA

Kungiyar Ecowas ta ce ta shirya tsaf wajen shawo kan matsalolin ayyukan ta’addanci a shiyyar Afrika ta yamma

2023-07-19 13:48:58 CMG Hausa

 

Shugaban kungiyar Ecowas kuma shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya tabbatar da cewa kungiyar ta samar da wasu sabbin matakan da za su shawo kan kalubalen tsaro da ake fuskanta a yammacin Afrika.

Ya tabbatar da hakan ne jiya Talata lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Nijar da Benin da kuma Guinea-Bissau a fadarsa dake birnin Abuja. Ya ce yanzu haka kungiyar ta sake fasalta hanyoyin samar da kudade domin daukar dawainiyar yakar ayyukan ta’addanci a shiyyar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.//////

Shugaba PatriceTalon na jamhuriyar Benin da Umaru Sissoco na Guinea-Bissau da kuma Mohamed Bazoum na jamhuriyar Nijar sun shafe sa’o’i suna ganawar sirri da shugaban na tarayyar Najeriya kuma shugaban kungiyar ta Ecowas.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, shugaba Bola Ahmad Tinubu ya ce, hakika zaman taron nasu ya yi ma’ana matuka domin kuwa ya bijiro da wasu managartan tsare-tsare da za su taimaka wajen samar da dauwamammen zaman lafiya a kasashen dake yammacin Afrika baki daya.

Shugaba Tinubu ya ce, yana da yakinin cewa kasashen dake kungiyar suna da karfin arzikin da za su yaki ta’addanci a kowanne mataki, ta hanyar samar da asusun musamman.

Da yake karin haske a kan batutuwan da taron ya zartar, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta ECOWAS Dr. Omar Alieu Touray ya ce, an yanke shawarar shugaban jamhuriyyar Benin Mr. Talon zai fara wani rangadi zuwa kasashe uku na Afrika a madadin sauran shugabannin kasashen dake cikin kungiyar.

Ya kara da cewa, dukkannin shugabannin uku da suka halarci taron na jiya Talata bakin su ya zo daya a kan tabbatar da samuwar gwamnatin damokradiyya a kasashen da har yanzu ake fama da rikicin siyasa wato Mali, Burkin Fasso da kuma Guinea.

“Shugabannin sun jaddada aniyarsu na gaggawar samar da tabbataccen mulkin demokuradiyya a kasashen nan uku da ake rikici, kuma wajibi ne kowace kasa a cikin kasashen uku su bi tsari da ka’idojin da kungiyar ECOWAS ta shimfida wajen mika mulki, a nata bangaren kungiyar ta Ecowas za ta bayar da tallafi wajen gudanar da sahihin zabe a dukkan kasashen.”

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta Ecowas ya ce, taron ya kuma amince da amfani da dakarun mambobin kasashe wajen yaki da ayyukan ta’addanci a shiyyar, kuma za a cimma hakan ne ta amfani da kudaden hadaka da kasashen suka samar, sai dai ya ce kungiyar za ta yi marhabin da duk wani gudummawar kudi daga hukumomi da kungiyoyin kasa da kasa na duniya. (Garba Abdullahi Bagwai)